Home Labarai Da duminsa: Buhari ya nada mai shekaru 40 a matsayin shugaban EFCC

Da duminsa: Buhari ya nada mai shekaru 40 a matsayin shugaban EFCC

36
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC da ke binciken masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annaci. DCL Hausa ta karanta sanarwar da mai ba shuagaban Najeriya shawara ta fuskar yada labarai, Femi Adeshina ya fitar a shafins ana Facebook a wannan Talata inda ya ce tuni Shugaba Buhari ya tura da sunan Abdulrasheed Bawan zuwa majalisar dattawan kasar domin ta tabbatar da shi.

Rahotanni sun nuna cewa Abdulrasheed Bawa na cikin jami’an hukumar na farko da suka fara yin aiki a EFCCin kuma ana yabonsa da cewa ya san aikinsa a wurin gano masu cin hanci da karbar rashawa.

Tun a ranar 10 ga watan Yulin 2020 Shugaba Buhari ya sanar da dakatar da Tsohon Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu bisa wasu zarge-zarge.

 

Buhari ya dakatar da Magu daga shugabancin EFCC

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply