Kotun daukaka kara da ke Abuja a Nijeriya, ta bukaci a aiwatar wa da Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda kotun farko ta zartas.
Maryam Sanda dai ita ce matar nan da ta kashe mijinta Bilyaminu kuma a karshen watan Janairu na 2020 kotu ta yanke mata hukuncin kisa amma sai ta shigar da kara inda take so a hana aiwatar da hukuncin kisan da wata babbar kotu ta yanke mata a baya.
DW Hausa ta ruwaito kotun ta Abuja, ta ce ta amince da hukuncin kisa ta hanyar rataya da babbar kotun ta yanke mata.
Labarai Masu Alaka da Wannan:
Kotu ta tabbatar Maryam Sanda ce ta kashe mijinta
Hukuncin Maryam Sanda: Afuwa ko Aiwatarwa?
Dole ne a yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa – Rundunar ‘Yan Sanda
AN SAKE AIKATAWA: Wata mata ta kashe mijinta da wuka a jihar katsina
