Home Kasashen Ketare Da gaske sojoji na cin zarafin farar hula a Nijar?

Da gaske sojoji na cin zarafin farar hula a Nijar?

148
0

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar farfesa Issoufou Katambe ya nisanta sojojin kasar da zargin da hukumar kare hakkin dan Adam CNDH ta yi musu na kashe fararen hula.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ministan ya ce gwamnati da ma’aikatar tsaron kasar na kara jaddada goyon bayan ta ga jami’an tsaron tare da kara tabbatar da cewa sojojin na gudanar da aikin su ne cikin kyautata doka da kare hakkin farar hula.

Ya ce gwamnati na kira ga al’ummar kasar da su san cewa jami’an tsaron na gudanar da aikin su ba dare ba rana domin kare su da kuma kasar bakidaya.

A makon da ya gabata ne hukumar da ke fafitikar kare hakkin dan Adam (CNDH) a jamhuriyar ta fitar da wani sakamakon bincike da ta yi a yankin jihar Tillaberie da a cikin sakamakon ta zargi sojojin kasar da amfani da karfin bindiga wajen cin zarafi da ma kashe fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply