Tsohon babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Lt Gen Tukur Yusuf Buratai yace da wahala a kawo karshen ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram nan da shekaru 20.
Buratai a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dokoki ta kasa mai kula da harkokin kasashen waje a lokacin da ya je domin tantance a nada shi mukamin jakada, yace da dadewa ‘yan ta’adda sun yi wani kulli da dauki tsawon lokaci kafin a iya warware shi.
Yace duk da sojojin Nijeriya da takwarorinsu na kasashe makwabta, Kamaru da Chadi da Nijar na samun nasarori, amma dai aikin zai musu wahala su kammala yaki da ta’addanci.
