Akwai yiwuwar ɗan wasan tsakiyar Arsenal Thomas Partey zai buga wasan da ƙungiyar za ta kara da Manchester United a ranar Asabar.
Ɗan wasan Kasar Ghana, ya faɗi ne bayan dawowa hutun rabin lokaci a wasan da Gunners ta doke Southampton da ci 3-1, wanda hakan ya sa fargabar Partey ba zai buga wasan hamayyar da za a yi a filin Emirates ba.
Da yake magana da ƴanjarida a ranar Alhamis Manajan Arsenal Mikel Arteta ya ce ba shi da tabbas kan ko Partey da Emile Smith Rowe za su buga a wasan na ranar Asabar.
Saidai wata majiya ta kusa da ɗan wasan ta shaidawa goal.com cewa ɗan wasan ya warke kuma zai kasance a karawar ƙungiyar da ɓangaren Ole Gunnar Solskjaer.
