Shugaban kungiyar Izala a Nijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shawarci malaman addinin musulunci da su karkatar da da’awar su kan ingancin zaman lafiya, domin yin hakan zai zama gudunmawar su wajen wanzar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci hakan ne ya yin jagorancin uwar kungiyar ta kasa zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna, inda ya ce kungiyar Izala a shirye ta ke tsaf wajen bayar da gudunmawa kan yadda za a samar da zaman lafiya mai dorewa.
