Home Sabon Labari Budurwar Femi Kayode ta haifa masa jariri

Budurwar Femi Kayode ta haifa masa jariri

173
0

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a Nijeriya, Femi Fani-Kayode, ya samu karuwa ta  da namiji a ranar Asabar din nan. Sai dai wasu na cewa  tsohon ministan ya samu jaririn ta hanyar dadaddiyar budurwarsa wace kawo yanzu jama’a ba ta shaida bikin aurensu ba.

DCL Hausa ta shaida sakon taya murna da samun haihuwar da dan siyasar na jam’iyyar PDP ya yi wa kansa a shafinsa na Twitter.

“Maraba da zuwa duniya! Hakika kai babbar ni’ima ce.  Ina matukar farin ciki da kuma alfahari da zuwan ka”. Inji Femi Kayode.

Mista Fani-Kayode ya kuma tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES, sai dai ya ki ya bayyana asalin mahaifiyar jaririn, yana mai cewa bai san bayyana sunanta don kada jaridu su sanya ta a gaba su yi ta buga labarai a kanta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply