Home Kasashen Ketare Dakarun Nijar sun fatattaki yan ta’adda 120 a Tillaberi

Dakarun Nijar sun fatattaki yan ta’adda 120 a Tillaberi

71
0

A wata sanarwa da aka karanta a gidan radio da talabajin din kasar ne gwamnati jumhuriyar Nijar ta bayyana cewa dakarun kasarta hadin guiwa da rundunar tsaron BARKANE ta Faransa sun yi nasarar kakkabe ‘yan ta’adda akalla 120.

Sanarwar da Ministan Tsaron Kasar Farfesa Issoufou Katambé ya fitar a ranarJuma’a, ta ce sojojin hadin guiwar sun samu wannan nasara daga farkon wannan wata na Fabrairu zuwa yanzu a dajin da ke yankin Tillaberi iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso

Har ila yau sanarwar ta ce babu wanda ya rasa ransa daga bangaren sojojin. ministan kuma ya jinjina ma kokarin jami’an tsaro tare da karfafa musu guiwa.

Wannan nasara ta biyo bayan wani taron da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya jagoranta a birnin Peau na kasar tasa tare da Shugabannin Yankin Sahel din nan guda 5 dan sake damarar yakin ta’addanci a yankin a watan Janairun da ya gabata.

Sojojin Nijar 175 ne dai suka hadu da ajalinsu a tsakanin watan Disamba da Janairun da suka gabata sakamakon hare-haren da suka fuskanta daga ‘yan ta’addar duk a yankin Tillaberin, lamarin kuma da ya kai gwamnatin yi ma Majalisar Tsaronta garanbawul.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply