Home Labarai Dakatar da hafsoshin tsaro: Fadar shugaban kasa ta maida wa Majalisa martani

Dakatar da hafsoshin tsaro: Fadar shugaban kasa ta maida wa Majalisa martani

153
0

Fadar shugaban kasa ta ce ta saurari matakin majalisar dattawa na kiran hafsoshin tsaron su yi murabus, fadar na mai bada tabbacin cewa shugaba Buhari zai yi komai da ya dace don ci gaban kasar a ko yaushe.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Saidai Adesina, ya ce nadawa ko sauke hafsoshin tsaron hakki ne da ya rataya a wuyan shugaban kasa, kuma shugaba Muhammadu Buhari zai yi komai do kariyar muradun kasar a ko yaushe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply