Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi “Dala bilyan 12 Najeriya ke asara sakamakon rikicin makiyaya da manoma”

“Dala bilyan 12 Najeriya ke asara sakamakon rikicin makiyaya da manoma”

122
0

Dala bilyan 12 Najeriya ke asara sakamakon rikicin makiyaya da manoma a duk shekara.

Daraktan kungiyar sa kai ta Mercy Corps, Ndubisi Anyanwu, a ranar Talata ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai bayan ganawa da jami’an gwamnati a birnin Makurdi jihar Taraba.

“Mun yi kiyasin asarar akalla $12b a kowace shekara sakamakon rikicin makiyaya da manoma. “Wannan wani babban al’amari ne kuma da zai iya shafar kasar baki daya,” a cewarsa.

Anyanwu shaida wa jaridar Muryar ‘Yanci cewa akwai bukatar a mayar da hankali kan rikici tsakanin makiyaya da manoma, yana mai cewa wannan ne ma dalilin da ya sa kungiyar ta shiga cikin lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply