Home Sabon Labari #DalibanKankara: Matasan arewa za su yi zanga-zanga zuwa Daura, mahaifar Buhari

#DalibanKankara: Matasan arewa za su yi zanga-zanga zuwa Daura, mahaifar Buhari

173
0

Gamayyar kungiyoyin arewacin Nijeriya ta bayyana cewa reshinanta na jahohi za suyi tattaki zuwa Daura, mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari don yin zanga-zanga kan sace dalibai da aka yi a karamar hukumar Kankara da ke kudancin jihar Katsina. Yawan daliban da kawo yanzu ake zullumin suna hannun ‘yanbindigar ya haura  300, acewar hukumomi.

 

‘Yanbindigar sun kai hari ne a makarantar sakandire ta garin Kankara a a ranar Jumma’a da daddare, inda suka sace daliban jim kadan bayan saukar shugaban Nijeriya a mahaifarsa Daura a da ke arewacin jihar ta Katsina.

 

Mai magana da yawun kungiyar ta gamayyar kungiyoyin arewa Abdul-Azeez Suleiman ya bayyana cewa yan kungiyar tasu za ta isa garin shugaban kasar  kuma za ta yi ‘zaman dirshen’ har sai an kubutar da daliban da maharani suka kwashe..

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply