Home Sabon Labari Dalilin da ya sa na rungumi Gwamna Masari – Shema

Dalilin da ya sa na rungumi Gwamna Masari – Shema

1709
0
Ibrahim Shehu Shema
Ibrahim Shehu Shema

Tsohon Gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya ce ya dauki matakin gaisawa da Gwamnan jihar mai ci Alhaji Aminu Bello Masari domin sun hadu a wurin taron masarauta.

Sai dai ‘yanjarida sun tambaye shi, me ya sa duk haduwar da ya ke yi da Gwamna Masari ba a taba ganin sun rungumi juna ba? Sai tsohon gwamnan ya ce “saboda dabi’a irin ta dan’Adam; ba mu taba zama kusa da kusa kamar lokacin ba”.

Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne a ya yin taron jami’iyyar PDP reshen jihar Katsina da aka gudanar a baya-bayan nan, inda shi da kan shi ya kama murmushi da ya ga ‘yanjarida sun dage sai ya yi musu bayani kan dalilan rungumar junar da suka yi da Gwamnan jihar Aminu Masari, wanda a baya ake ganin babu wanda ya raga wa wani a fagen siyasa.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Aminu Bello Masari na APC ne dai ya karbi mulkin jihar Katsina a hannun Ibrahim Shehu Shema na jam’iyyar PDP a 2015 bayan ya kammala shekaru takwas, amma dan takarar PDP a 2015 din ya gaza samun nasara.

Da hawan Gwamna Masari na APC a 2015 ya fara kaddamar da bincike inda gwamnatinsa ta ke zargin tsohon gwamna Shema ya wawuri dukiyar jihar, abin da ya haifar da zazzafar adawa a tsakanin bangarorin biyu.

Sai kuma ga shi a karshen mako an dauke su hoto sun rungume juna, har ma Gwamna mai ci yana yi wa Ibrahim Shema ‘rada’ a kunne. Wannan lamari dai da alama zai ci gaba da daure wa ‘yan jihar ta Katsina kai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply