Home Coronavirus Dalilina na rage Ma’aikata a kamfanin Gotel–Atiku

Dalilina na rage Ma’aikata a kamfanin Gotel–Atiku

87
0

Tsohon mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubarka, ya kori ma’aikata 46 a Ranar 1 ga Mayu wadda ita ce ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin bikin ranar ma’aikata.

Atiku dai shi ne wanda ya kafa kamfanin na Gotel Communications, wanda su ke watsa shirye-shiryen su na gidan talabijin da rediyon daga Yola, babban birnin jihar Adamawa.

A cewar tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar yace korar ma’aikatan 46 na alaƙa da rashin isassun kuɗaɗen gudanar al’amura a kamfanin.

Ya kara da cewa annobar cutar Corona ta haifar da rugujewar tattalin arzikin duniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply