Home Labarai Dalilinmu na rage albashin ma’aikata – Gwamnatin Kano

Dalilinmu na rage albashin ma’aikata – Gwamnatin Kano

265
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta soke yin amfani mafi ƙarancin Albashi na ₦30,000 ne saboda matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

Mai ba gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai, wanda ya bayyana haka a ranar Laraba, ya ce gwamnatin jihar ba za ta iya ci gaba da biyan sabon tsarin albashin ba, saboda kuɗin da take samu sun ragu.

Rahotanni dai sun nuna kimanin ma’aikata 55,505 wannan mataki ya shafa daga ranar 31 ga watan Disambar 2020, ciki har da masu riƙe da muƙaman siyasa da Gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply