Kwamitin yaki da coronavirus a jahar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar ya karbi wasu kayayyakin yaki da cutar a jihar. Kayayyakin kuwa sun kunshi na’urorin taimakon numfashi guda biyar.Ma’aikatar Lafiyar Kasar ce ta kawo wa jihar wannan dauki.
Ministan Lafiya Nijar ne daman ya yi alkawalin kawo na’urorin a yayin wata ziyara da ya kawo jahar a kwanaki baya. Shugaban kwamitin magance coronavirus a Damagaram Haru Maman ne ya karbi kayayyakin.
Jahar Damagaram dai ita ce jaha ta biyu da ke da mafi yawan masu dauke da corona a Jamhuriyar Nijar inda a yanzu haka take da mutum 123 a cikin mutum 937 da suka kamu da cutar a kasar kawo yanzu. Jami’ar John Hopkins ta Amirka ta ce mutum 60 sun mutu cikin wannan adadi yayin da 764 suka warke daga cutar.

A baya-bayan nan dai jahar na zama kan gaba wajen samun mutane sabbin kamuwa inda ko a sakamakon ranar Juma’ar nan ma cikin mutane 13 da aka samu sabbin kamuwa 7 cikin su ‘yan jahar Damagaram ne.
A daya bangare kuma babban birnin Yamai da a yanzu ke kan gaba a mafi yawan masu dauke da cutar a baya bayan nan birnin na samun ragowar sabbin kamuwa inda a kwanakin nan sai da aka kwashe kwanaki 4 ba tare da an samu ko mutum 1 sabon kamuwa ba.
