Home Sabon Labari Dambarwar siyasa: Dino Melaye ya yi fatali da soke zabensa da kotu...

Dambarwar siyasa: Dino Melaye ya yi fatali da soke zabensa da kotu ta yi

78
0

Rahma Ibrahim Turare.

Sanata Dino

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Arewa a jihar Kogi Sanata Dino Melaye, ya yi watsi da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke akan nasarar da ya samu ta lashe zabe. Kotun dai a ranar juma’a ta sanar da soke zabensa ta kuma bukaci a sake sabon zabe.

Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa wannan hukunci kin gaskiya ne karara, kuma kotun daukaka kara za ta rushe shi da zarar ya daukaka kara.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, yace yanke hukuncin wani shiri ne na son zuciya don kawai a dakile kudirinsa na son fitowa takarar gwamna a jihar Kogi.

Ya kara da cewa yana so ‘yan Nijeriya su sani cewa akwai tsabagen rashin adalci a hukuncin da shugaban alkalan kotun sauraren kararrakin zabe ya yanke.

Sanata Dino Melaye

“Ina so in kara tabbatar da cewa wannan hukuncin ba zai yi tasiri ba a kotun daukaka kara. Saboda a matsayina na dalibin shari’a wanda ya san duk wani hukuncin da bai cika sharudda ba, to wannan hukuncin rusashe ne” inji shi.

Dino Melaye yace jira ya ke yi majalisar dattawa ta dawo daga hutun da ta tafi domin a tabbatar da cewa har yanzu shi ne danmajalisar dattawa mai ci ba korarre ba, kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta sanar.

Ya yi zargincewa akwai tsoro a tattare da gwamnan jihar ta Kogi Yahaya Bello na barin gidan gwamnati sai ya tabbatar wa mutanen jihar kogi cewa za su yi ban kwana da yunwa, talauci da kuma mulkin kama karya da ake yi musu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply