Home Sabon Labari Damben Boxing: Ruiz-wilder ya sake yin nasara akan Joshua a tirmi na...

Damben Boxing: Ruiz-wilder ya sake yin nasara akan Joshua a tirmi na biyu.

89
0

Daga Rahama Ibrahim Turare

 

Dan damben boxing Anthony Joshua ya sadakas, a ya yin da ya sha kasa a damben da suka kafsa da Ruiz-wilder Jr, a karo na biyu.

A watan da ya gabata ne Ruiz Jr ya karbe kyautukan da ke hannun Joshua da suka hada IBF, WBA da WBO, abin da ya bakanta ran Joshua matuka, tare da raunana kyakkyawar fatarsa ta ci gaba da rike kambun danben.

Joshua dai yana tunanin tafiya kai tsaye ga gasar damben ta gaba domin kokarin shi na sake kwato kambun darajojin shi na duniya daga hannun Ruiz Jr.

Bayan dai samun nasara da Ruiz ya yi, ya bugi kirjin cewa ya zuwa yanzu kanwa ta kas tsami….kwarnafi ya kwanta, maganar da ta kara sosa ran Joshua matuka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply