Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wani dan Nijeriya, Olusegun Adejorin, hukuncin daurin watanni 96 (shekaru takwas) a gidan yari, bayan samunsa da laifin amfani da dabarun damfara ta yanar gizo wajen karkatar da sama da dala miliyan 7.5 daga wasu kungiyoyin agaji guda biyu.
Alkalin kotun gundumar Maryland a Amurka, Theodore Chuang, ya yanke wa Adejorin mai shekaru 32 wannan hukunci, tare da karin wa’adin sanya ido na shekaru uku bayan ya kammala zamansa a gidan yari, sakamakon samunsa da laifukan damfarar yanar gizo, satar bayanan sirri, da kuma kutse a na’urorin kwamfuta ba tare da izini ba.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ce ta kamo Adejorin daga kasar Ghana zuwa Amurka a watan Agustan 2024 domin fuskantar shari’a, inda kotu ta same shi da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su a watan Disambar 2025 bayan shafe kwanaki shida ana sauraron shari’ar.
A cewar bayanan da aka gabatar a gaban kotu, Adejorin ya yi kutse cikin asusun sakon intanet (email) na ma’aikatan wata kungiyar agaji da ke New York, inda ya rika nuna kansa a matsayin daya daga cikin ma’aikatan tare da ba da umarnin cire kudade daga wata kungiyar agaji ta daban da ke Maryland.
Binciken ya nuna cewa ya kuma yi kutse a asusun kungiyar ta Maryland domin aika sakonnin bogi na amincewa da cire kudaden, lamarin da ya sa aka karkatar da sama da dala miliyan 7.5 zuwa wasu asusun banki na daban da ba na kungiyar ba.
Lauyar Gwamnatin Amurka a gundumar Maryland, Kelly Hayes, tare da babban jami’in FBI a ofishin Baltimore, Jimmy Paul, sun yaba da hadin gwiwar da aka samu tsakanin hukumomin Amurka da na kasar Ghana wajen mika wanda ake zargin domin fuskantar shari’a.
