Abdullahi Garba Jani
Ambaliyar ruwa ta ja wasu yara 3 a yankin Sa’idawa da ke karamar hukumar Danbatta ta jihar Kano biyo bayan wani mamakon ruwan sama.
Jami’in watsa labaran karamar hukumar Malam Nura Umar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ruwan ya tafi da yara ‘yan mata 2 da yaro namiji daya ta dalilin wannan mamakon ruwan sama.
Ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta shafi al’ummomin Fagwalawa, Makera, Turu da Unguwar Mahuta, kuma ta lalata kadarori da dama.
Mukaddashin shugaban karamar hukumar Danbatta, Malam Musa Danbatta, a lokacin da ya ke ba da tallafi ga al’ummomin da abin ya shafa, ya jajanta musu kan wannan lamari da ya faru da su.
Ambaliyar ruwa dai na sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dukiyoyi. Ko a kwananan a jihar Jigawa, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar lalacewar gonaki masu murabba’in kadada 12,000.
