Sakamakon gwaji ya nuna Mohammed Atiku-Abubakar ya warke daga cutar Coronavirus. Mohammed
Mohammed wanda ɗa ne ga Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya shafe kwanaki 40 a killace kuma an ba shi kulawa bayan ya harbu da cutar Covid-19 a wani asibiti da ke Gwagwalada a Abuja inda ake kulawa da masu Coronar.
Ana zargin cewa Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya samu cutar Covid-19 ne daga wurin Mohammed Atiku bayan wata ganawa da suka yi a cikin jirgin sama. Sai dai yanzu dukkansu sun warke.
