Home Labarai Dan majalisa ya bindige dan fashi a Sokoto

Dan majalisa ya bindige dan fashi a Sokoto

57
0

Danmajalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar wakilai, Abdullahi Salame ya bindige wani dan fashi har lahira, yayin da ya rauna ta abokansa a lokacin da suka je gidan shi da ke unguwar Bado a Sokoto da karfe ukun dare don yi masa fashi.

A daren  Juma’ar nan ne, misalin karfe 3 na dare ‘yan bindiga suka farmaki gidan Hon. Abdullahi Balarabe Salame, dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Goronyo.

Wasu majiyoyi sun ce bayan bata kashi tsakanin ‘yan bindigar da masu gadin gidansa an yi nasarar harbe daya daga cikin ‘yan bindigar tare da raunata wasu.

Kokarin jin ta bakin Rundunar ‘yansandan jihar Sakkwato ya faskara zuwa lokacin haɗa wannan labari.

Birnin Sakkwato dai na kara fuskantar matsalolin rashin tsaro inda ake afka wa gidajen mutane cikin dare, inda hakan ta faru kusan unguwanni hudu na tsakiyar Birnin, yanzu hakama dai mutane na zama cikin fargaba idan dare ya yi, takai ga ko sallar Asuba wasu sun daina fita saboda gudun abunda ka iya zuwa ya komo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply