Home Labarai Dan majalisar Tarayya ya tsallake rijiya da baya a Sokoto

Dan majalisar Tarayya ya tsallake rijiya da baya a Sokoto

51
0

A daren  Juma’ar nan ne, misalin karfe 3 na dare ‘yanbindiga suka farmaki gidan Hon. Abdullahi Balarabe Salame, dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Goronyo.

Wasu majiyoyi sun ce bayan bata kashi tsakanin ‘yanbindigar da masu gadin gidansa an yi nasarar harbe daya daga cikin ‘yanbindigar tare da raunata wasu.

Kokarin jin ta bakin Rundunar ‘yansandan jihar Sakkwato ya faskara zuwa lokacin haɗa wannan labari.

Birnin Sakkwato dai na kara fuskantar matsalolin rashin tsaro inda ake afka wa gidajen mutane cikin dare, inda hakan ta faru kusan unguwanni hudu na tsakiyar Birnin, yanzu hakama dai mutane na zama cikin fargaba idan dare ya yi, takai ga ko sallar Asuba wasu sun daina fita saboda gudun abunda ka iya zuwa ya komo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply