Home Labarai Dan Nijeriya ya zama shugaban jami’a a Birtaniya

Dan Nijeriya ya zama shugaban jami’a a Birtaniya

134
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murna tare da bayyana jin dadinsa sakamakon nadin da jami’ar Leeds Trinity University da ke kasar Birtaniya ta yi ma Farfesa Charles Egbu dan asalin jihar Anambra a matsayin sabon shugaban jami’ar.

Sakon na taya murna na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da kuma hulda da jama’a Femi Adesina ya fitar a ranar Juma’a a shafinsa na Facebook.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi farin ciki kwarai da da jin labarin nadin na Farfesa Charles Egbu.

Farfesa Charles Egbu ya kasance bakar fata na farko da aka nada shugabancin wannan fitacciyar jami’a ta Birtaniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply