Home Sabon Labari Dan sanda ya bindige kansa bayan ya harbe wasu abokan aikinsa

Dan sanda ya bindige kansa bayan ya harbe wasu abokan aikinsa

93
0

Taskar Guibi: Karanta Takaitattun Labaru na 22.12.2019

 

 

Aalaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da biyar ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyu ga watan Disamba na 2019.

1. Jiya aka gudanar da taron kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka wato ECOWAS a takaice a Abuja karkashin jagorancin shugabanta na yanzun shugaban kasar Nijar. Inda shugaban kasa Buhari ya nuna cewa babban kalubalen da ke ci wa kungiyar tuwa a kwarya shi ne ‘yan ta’adda, har da waiwayar kashe sojojin Nijar su saba’in da daya da aka yi a farkon watan nan.

2. Ministar kudi ta yi wa kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban kasa ya sa wa hannu gwari-gwari.

3. Wani sifeta na ‘yan sanda a Abuja Marcus, ya bindige wani dan sanda ya mutu, ya sake bindige wani dan sanda amma bai mutu ba, ya juya ya bindige kansa ya mutu.

4. Sojoji sun soma janyewa a hankali daga jihar Binuwai da Taraba da Nasarawa saboda daidaiton al’amuran tsaro.

5. Kwastam sun kutsa kasuwar Mubi suka kwace shinkafa ‘yar waje.

6. Ma’aikatan gwamnatin tarayya na ci gaba da dakon ariyas na sabon albashi da aka musu alkawarin za a biya nan da kafin karshen watan nan na Disamba da zai kare nan da kwana tara.

7. Amurka ta sa Nijeriya cikin jerin kasashen da take sanyawa ido bangaren kyamar akidar mutum.

Af! A dai-dai lokacin da ake ci gaba da neman mutane biyu da aka sace a yankin Birnin Gwari, da ke jihar Kaduna, da uku da aka sace a yankin Sabon Tasha da ke cikin garin Kaduna, a cikin garin Kudan da ke jihar ta Kaduna an bi Alhaji Magaji Maigyada har gida an yi kidinafin dinsa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply