Home Sabon Labari Dan sanda ya bindige matarsa a Nijeriya

Dan sanda ya bindige matarsa a Nijeriya

63
0

Ana zargin wani jami’in dan sanda mai muƙamin insifeta da ke aiki a garin Kaima a jihar Bayelsa mai suna Tuddy Warebayigha ya kashe matarsa, Chairing Tuddy. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a bayan wara hatsaniya da ta kaure a tsakaninsu.

Tuddy dai ya ja matar ta shi zuwa wata gonarsu da ke a unguwar Sampou a Karamar Hukumar Kolokuma / Opokuma inda ake zargin anan ne ya harbe ta. Bayan da labarin ya bulla daga bisani sai aka garzaya da ita asibiti, inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Asinim Butswat, ya ce tuni dai hukumarsu ta damke wannan jami’i na su inda ake tsare da shi a sashen binciken manyan laifuka na jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply