Home Sabon Labari Kukan Zuci Dan shekara 18 ya yi wa kakarsa ‘yar shekara 70 fyade a...

Dan shekara 18 ya yi wa kakarsa ‘yar shekara 70 fyade a Filato

130
1

Jami’an ‘yan sandan jihar Filato da ke Najeriya sun tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 18 bayan ya yi wa kakarsa mai shekaru 70 fyade. Jami’an ‘yan sandan sun ce, matashin mai suna Marvellous Luka na zaune ne a kauyen Dangu-gu da ke yankin kudancin Ampang na Mangu a jihar ta Filato, kamar yadda gidan rediyon Faransa ya walalfa a shafinsa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, tuni aka tuhumi matashin kuma nan gaba kadan za a gabatar da shi a gaban babbar kotun Pankshin. Jaridar Daily Trust ta ce Luka ya shiga hannu ne bayan da wasu matasa suka gane abin da yayi inda suka shiga cikin gari suka nemo shi su ka mika wa ‘yan sanda.

Matashin ya ce sha’awa ce ta kama shi ya kuma rasa inda zai kawar da sha’awar sai shaidan ya sa shi farma kakarshi mai shekaru 70. Ya ce lallai kakar tashi tayi kokarin bijirewa amma ya nuna mata karfi ya samu abin da ya ke so.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply