Home Kasashen Ketare Dan wasan Man City Silva ya koma Real

Dan wasan Man City Silva ya koma Real

193
0

Kwanaki biyu bayan fitar da kungiyar Man City daga cin kofin zakarun turai, dan wasan tsakiyar kungiyar David Silva ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da kungiyar Real Sociedad ta kasar Spain da ke buga wasanninta a ajin kwararru, La Liga.

David Silva ya shafe shekaru goma yana buga wasannin Kungiyar Manchester City, ya kuma yi zamani da yan wasa da masu horaswa daban-daban.

Silva dan asalin kasar Sifaniya, ya taimaka wa tsohuwar kungiyarsa ta Man City lashe kofin firimiya guda 4, da kofin FA 2 da league cup guda 5.

Wasan shi na karshe da ya buga wa kungiyar, shi ne wasan zagayen dab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai ranar Asabar da suka kara da kungiyar Lyon a Lisbon.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply