Ahmadu Rabe Yanduna/dkura
Kungiyar Real Madrid ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis cewa dan wasanta na tsakiya Isco ya samu rauni. Sai dai ba ta bayyana kwanakin da dan wasan zai dauka ya na jinya ba.

Isco na daya daga cikin ‘yan gaba-gaba a jerin ‘yan wasan da kocin Real Madrid Zinadine-Zidane ke amfani da su a kusan kowanne wasa. Ana zullumin akwai yiyuwar dan wasan zai iya rasa wasan Real Madrid da Villarreal da kuma wasa tsakanin Real Madrid da Levante ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa.
Isco ya shiga sahun wasu daga cikin yan wasan Madrid kusan 5 da yanzu haka ke jinya, wadanda suka hada da James Rodriguez, Eden Hazard da Marco Asensio da kuma Rodrygo sai kuma Brahim Diaz.
