Home Kasashen Ketare Dangantaka na kara tsami tsakanin Amurka da China

Dangantaka na kara tsami tsakanin Amurka da China

119
0

Kasar China ta ba da umurnin rufe ofishin jakadancin ta da kasar Amurka da ke birnin Chengdu, biyo bayan yawaitar samun rikicin difilomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce matakin da suka dauka yana a matsayin martani ga Amurka bayan da suka rufe masu ofishin jakadancinsu da ke jihar Texas.

Shugaba Trump ne ya bada umurnin da a rufe ofishin na kasar China a yau Juma’a, bayan da suka yi la’akari da cewa ofishin na kasar China na leken asiri ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply