Home Kasashen Ketare Dangantaka tsakanin Jamus da Russia na nema ta yi tsami

Dangantaka tsakanin Jamus da Russia na nema ta yi tsami

111
0

Dangantaka tsakanin kasar Russia da Jamus na dada samun tasgaro bayan da gwamnatin kasar ta zargi shugaba Vladimir Putin da hannu a sanya wa shugaban ‘yan adawar kasar Russia Alexei Navalny guba.

Kasar Jamus dai ta kudiri aniyar daukar matakai masu tsauri idan har fadar Kremlin ta mayar da martani marar dadi kan zarginta da hannun akan rashin lafiyar Madugun adawar kasar.

Sai dai kasar Rasha ta yi watsi da zargin da ke alakanta shugaba Putin da yunkurin halaka Navalny ta hanyar sanya masa guba.

Yanzu haka Navalny na kwance a wani asibiti a birnin Berlin na kasar Jamus tun bayan da ya kama rashin lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply