DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBabban Labari Dangote ya fadi dalilin da ya sa fetur ya yi tsada a...

Dangote ya fadi dalilin da ya sa fetur ya yi tsada a Nijeriya

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ci gaba da fasakwaurin man fetur zuwa ƙasashen maƙwabta na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa farashin man yake da tsada a Nijeriya.

Dangote ya bayyana cewa farashin man fetur a ƙasashen maƙwabta ya zarce na Nijeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin ɗari, yana mai cewa wannan bambancin farashi yana ƙara bai wa masu fatauci da ’yan fasakwauri kwarin gwiwa wajen fitar da man daga Nijeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Talata, yayin da yake magana kan farashin fetur da kuma samuwar man a kasuwa a daidai lokacin da ake fama da rikicin Gabas ta Tsakiya.

Dangote ya ce ba za a iya kallon farashin fetur a Nijeriya shi kaɗai ba tare da la’akari da farashin man a ƙasashen da ke makwabtaka da Nijeriya ba.

Ya ce idan aka kwatanta farashin fetur a Nijeriya da na ƙasashen da ke kusa da ita, za a ga cewa akwai babban bambanci, wanda ke ƙarfafa masu safarar man su fitar da shi daga ƙasar.

Ɗangote ya ce har yanzu ana samun yawan fasakwaurin man fetur da ake samarwa a Nijeriya zuwa ƙasashen maƙwabta.

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ke safarar man na iya sayen fetur a Nijeriya sannan su fitar da shi zuwa wata ƙasa, inda za su samu ƙarin kuɗi saboda bambancin farashin man.

Dangote ya bayyana cewa farashin fetur a wasu ƙasashen maƙwabta ya fi na Nijeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin ɗari.

Ya ce wannan babban bambancin farashi yana sa safarar fetur zuwa ƙasashen maƙwabta ta zama wata hanya da masu fasakwaurin ke ganin za su iya samun riba cikin gaggawa.

Dangote ya bayar da misalin Jamhuriyar Nijar, inda ya ce farashin fetur ya fi na Nijeriya da kusan kashi 20 zuwa 25 cikin ɗari.

Ya ce idan farashin fetur a Nijeriya ya kai Naira 1,350, farashin man a Nijar zai iya kasancewa sama da haka da kashi 20 zuwa 25 cikin ɗari.

A cewarsa, irin wannan bambancin farashi na iya sa mutum ya fi ganin ya fi masa riba ya fitar da man zuwa ƙasar maƙwabciya, maimakon sayar da shi a cikin Nijeriya.

Dangote ya yi tambayar irin kasuwancin da zai iya bai wa mutum damar samun riba kai tsaye da kusan kashi 25 cikin ɗari, yana mai cewa hakan na daga cikin abubuwan da ke ƙarfafa fasakwaurin fetur.

Ya bayyana yadda wasu ke iya ɗaukar man da ake zaton za su kai wani gari a cikin Nijeriya, amma daga baya su karkatar da shi zuwa kan iyaka domin sayarwa a ƙasashen maƙwabta.

A cewarsa, mutum na iya yin ikirarin cewa zai kai man zuwa Sakkwato, amma daga bisani ya kai shi Ilela da ke kan iyaka, inda zai sayar da shi ga masu siya daga ƙasar maƙwabciya.

Dangote ya ce wannan na iya rage yawan man da ya kamata ya kasance a kasuwar cikin gida domin amfanin ’yan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa matsalar ba ta tsaya ga tsadar farashin fetur kaɗai ba, domin rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya na iya haifar da wata matsala ta daban a kasuwar man fetur.

A cewarsa, babban abin da ya kamata a duba nan gaba shi ne ko za a samu isasshen man fetur a kasuwa, ba wai farashin man kaɗai ba.

Dangote ya ce rikicin Gabas ta Tsakiya na iya shafar kasuwannin makamashi na duniya, lamarin da zai iya yin tasiri kan samuwar da kuma farashin kayayyakin man fetur.

Sai dai ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa matatar man Dangote a shirye take ta ci gaba da samar da isasshen fetur domin biyan buƙatun kasuwar cikin gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata