Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fiye da Dala miliyan 800 da kamfanin Sinoma International Engineering Co. Ltd. domin faɗaɗa masana’antar simintinsa da ke Itori a Jihar Ogun, Nijeriya.
Ana sa ran hakan zai ninka yawan samar da simintin masana’antar daga tan miliyan shida zuwa tan miliyan 12 a duk shekara, lamarin da zai ƙara yawan samar da siminti a ƙasar.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, da shugaban kamfanin Sinoma, Lin Zhong, suka rattaba hannu kan takardar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Yarjejeniyar na ɗaya daga cikin manyan zuba jari da aka yi a fannin masana’antu a Nijeriya, musamman wajen bunƙasa masana’antar siminti.
Dangote ya bayyana cewa faɗaɗa masana’antar zai taimaka wajen ƙara yawan samar da siminti domin biyan buƙatun cikin gida da kuma na kasuwannin ƙasashen waje.
Ana sa ran wannan aiki zai samar da ƙarin guraben aikin yi tare da ƙarfafa sashen masana’antu da tattalin arzikin Nijeriya.
Bayan kammala aikin, ana hasashen Nijeriya za ta ƙara ƙarfafa matsayinta na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka masu samar da siminti da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, ana kallon haɗin gwiwa tsakanin Dangote Industries da Sinoma International Engineering a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa masana’antun cikin gida da bunƙasa ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
