Home Wasanni AFCON 2019: Dangote zai yi wa ‘yan wasan Najeriya kyauta

AFCON 2019: Dangote zai yi wa ‘yan wasan Najeriya kyauta

99
0
  1. ATTAJIRAN NAJERIYA SUN CE DUK KWALLON DA YAN SUPER EAGLES SUKA ZURA A RAGA TO ZA SU SAMI KYAUTAR SAMA DA NAIRA MILYAN 20.

Babban attajiri na Afrika Aliko Dangote ya bayyana a jiya da daddare cewa zai ba yan kwallon Najeriya kyautar Naira Milyan 18 akan kowace kwallo da suka ci abokanan karawarsu a ci gaba gasar cin kofin Afrika da ke gudana a kasar Masar.

Shi kuma a nasa bangaren shahararren mai kudi a kasar Yarbawa, Femi Otedola ya ce zai rinka ba yan super eagles Naira Milyan 9 akan kowace kwallo daya da suka zura.

Gidan Talabijin na Channels wanda ya bayar da wannan rahoto yace matakin na zama na karfafawa yan super eagles gwiwa don su sanya azama su dauki kofin gasar AFCON na wannan shekara.

Tirkashi, yaya kuke kallon wannan ruwan kudi akan yan kwallo?

#ZuD

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply