Home Labarai Dara ta ci gida: An saci mai garkuwa da mutane

Dara ta ci gida: An saci mai garkuwa da mutane

634
0

Mohammed Amodu, wanda ake zargin ya shahara wajen satar mutane don neman a biya shi kudin fansa shi ma ya shiga komar wata tawagar masu garkuwa da mutane inda suka sace shi har ta kai ga ya biya su kudin fansa har milyan 1 da dubu dari biyar da 55 (N1,555,000).

Mohammed Amodu
ya biya kudaden ne ga wasu gungun masu satar mutane na daban, wandanda wani mai suna Buba Babu, ke jagoranta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba, wanda ya gabatar da masu garkuwar tare da wasu masu aikata laifuka a ranar Litinin a Abuja, ya ce Buba ya yi kaurin suna wajen satar jama’a a kan manyan titunan da ke kusa da Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply