Home Labarai Dashen Itatuwa: Hukumar kula da gandun daji ta samar da wuraren dashe...

Dashen Itatuwa: Hukumar kula da gandun daji ta samar da wuraren dashe a jihohi 10 na Nijeriya

78
0

Daga Rahama Ibrahim Turare

Babban darakta a hukumar Mr.Andrew Adejoh ne ya bayyana hakan a wata tataunawa da ya yi da kamfanin Dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.    Ya ce a shekara ta 2018 hukumarsa ta samar da filaye masu yawan kadada dari takwas da saba’in da biyu a jihohi goma na Nijeriya.

Babban daraktan ya ce hukumarsa ta hada gwiwa da cibiyar nazarin gandun daji ta kasa don ganin an aiwatar da wannan yunkuri ka’in-da-na’in.

Hotan yadda ake sa ran gandun daji

Mr Andrew ya ce hukumarsa ta samu gudunmawar kudi daga asusu na musamman da aka ware don bunkasa dazuzzuka, Green Bond, wanda yanzu haka ke aiki a jihohi kamar haka; Gombe da Nasarawa da Kaduna da Enugu da Anambra  da Ondo da Ekiti da Oyo da Edo  da kuma babban birnin tarayya Abuja .

 

Hukumar tace tana ba jihohi kwarin gwiwa domin sake farfado da dashen itatuwa a wuraren da aka sassare itatuwan ,kuma tana kira ga duk yan Nijeriya da su sanya hannu acikin shirin dashen itatuwa. Ta kara da cewa dashen itatuwa zai matukar taimakawa wurin  inganta lafiya da mahalli.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply