Home Labarai Dattawan jihar Kano na neman Minista Fashola don gyara hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

Dattawan jihar Kano na neman Minista Fashola don gyara hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

72
0

Al’umomin da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi ta ratsa ta garuruwansu sun damu kwarai da gaske akan lalacewar da hanyar ta yi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya-NAN-ya ruwaito.

Alhaji Yunusa Haruna-Kauyu dan majalisa da ke wakiltar Gwarzo a jihar Kano ya ce sun shirya hada tawaga ta musamman da za ta gana da Ministan Ayyuka na Tarayya Babatunde Fashola don neman ya sa baki a gyara hanyar.

Tawagar da za ta je wurin Ministan za ta hada da Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano Alhaji Muazu Magaji da Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa Barau Jibrin-Maliya da kuma ‘Yan Majalisar Wakilai na wannan yanki”

Wadanda suka yanke shawarar zuwa wurin Ministan Tarayyar sun ce akwai bukatar Ministan ya san kuncin da jama’an yankin ke ciki saboda lalacewar hanyar. Sun ce akwai manyan ramuka masu yawa da ke tada wa direbobi hankali akan hanyar. Bayan haka sun ce hanyar ta lalace yadda gyaranta ta hanyar faci-faci ba zai iya magance lamarin ba. Sun ce za su bukaci gwamnatin tarayya ta daure ta sake shimfida sabuwar hanya don kyautata tattalin arzikin jama’a da rayukansu.

Mutanen jihohi hudu na Nijeriya da ‘yan jumhuriyar Nijar su ne suka fi amfani da hanyar ta Kano-Gwarzo-Dayi acewar dan majalisa da ke wakiltar Gwarzo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply