Home Kasashen Ketare David Silva zai yi ban kwana da gasar Firimiya

David Silva zai yi ban kwana da gasar Firimiya

236
0

A ranar Lahadin nan, dan wasan tsakiyar Manchester city David Silva zai buga wasan shi na karshe a gasar firimiyar Ingila bayan shafe shekaru goma yana buga wasannin na firimiya a kungiyar.

Silva dan asalin kasar Sifaniya, ya taimaka wa Man City ta lashe kofin firimiya guda 4, da kofin FA 2 da league cup guda 5.

Sai dai Silva zai ci gaba da zama a kungiyar har a kammala buga wasannin cin kofin zakarun turai da za a dawo a ranar Juma’a 7 ga Augustan da zamu shiga inda bayan kammala gasar zai yi ban kwana da kungiyar kwata-kwata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply