Abdullahi Garba Jani
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta na nan tana shirin maida wasu dazuka guda 5 zuwa wuraren kiwo don amfanin makiyaya.

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fadi haka a Abuja, inda yace gwamnatin jihar ta kafa kwamitin kwararru kan tsarin inganta gonaki da wuraren kiwo don makiyaya su inganta kiwonsu.
Yace sabon tsarin wurin kiwon zai kara bunkasa tattalin arzikin jihar, tare da dakile yawace-yawacen makiyaya daga arewa zuwa kudancin kasar.

Gwamna Ganduje yace hakan kuma zai taimaka wajen shawo kan matsalar rikice-rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.
Ya ce shirin zai samar da asibitocin kula da dabbobi da na kula da mutane, kasuwanni, makarantu da sassan inganta tsaro ta yadda makiyayan za su mori zaman wuraren kamar kowa.
