Home Sabon Labari Kukan Zuci DCL Hausa ta fito da shirin “ KUKAN ZUCI” don masu fama...

DCL Hausa ta fito da shirin “ KUKAN ZUCI” don masu fama da matsaloli

113
0

Sabon sashe na jaridar DCL Haua mai taken “ KUKAN ZUCI” ya zo don share muku hawayenku da baku shawarwari.

 

Abubuwa masu dadi da marasa dadi na ci gaba da wakana a gidajenmu da kasuwanninmu da ofisoshinmu da sauran wurare. Akwai matsalolin da saboda girmansu ba za kU so wani wanda ya sanku ya san kuna fuskantar su ba. Matsaloli da suka hada da neman yin fyade, ko neman yin lalata daga wurin wanda aka aminta da shi ko kuma a tsakanin saurayi da budurwa ko kuma abokan aiki. Akwai kuma wadanda rashin lafiya ce ta same su wadda jama’a ke kyamata kamar cutar HIV/AIDS ko Hepatitis, Sikila ko makamantansu amma kuma neman shawara ya zama jidali saboda girman matsalar da yadda al’umma ke daukar matsalar.

Matasa kuwa maza da mata masu fuskantar matsaloli a soyayya/ auratayya kuma muna dakonku ku turo mana da bayanan irin matsalolinku zamu rinka wallafawa.

Burinmu shi ne mu samar da dandali da jama’an da wata matsala ke cima tuwo a kwayar za su iya furzas da matsalar da ke damunsu da niyyar samun shawarwari daga jama’a wadanda idan aka yi amfani da su za su taimaka wurin gyara zamantakewa.

DCL Hausa za ta bayyana sirrinku ko sunayenku ga wani mutum?

A’a wannan kada kuji tsoro, ma’aikatanmu maza da mata ba za su bayyana sunayenku ko wallafa wasu bayanai ta hanyar da wanda ya sanku zai iya gane ku ba. Za mu rinka tantance wa wasu bayanai da gyara rubutu da cire wani bayanin da muka lura ka iya bayyana sunan mutum ko makamancin haka.

 

Jaridar DCL Hausa wadda ‘yan jarida da ke aiki a gida Nijeriya da kasashen ketare ke wallafawa ta fito da sabon tsarin da zammar karbar irin wadannan labarai daga gare ku ta adireshinmu na email ko kuma inbox dinmu. Ku aiko mana da irin wadannan labarai a : info@dclmedia24.com ko kuma dclhausa@gmail.com ko kuma ta inbox dinmu na jaridarmu ta DCL Hausa a shafinmu na facebook.

 

Sai mun ji daga gare ku

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply