Home Sabon Labari Delta: kotu ta soke zaben Sanatan Delta ta Kudu

Delta: kotu ta soke zaben Sanatan Delta ta Kudu

78
0

Abdullahi Garba Jani

 

Kotun sauraren kararrakin zabe ta ‘yan malajisar dokoki ta kasa da ke zamanta a birnin Asaba na jihar Delta, ta soke zaben Sanata James Manager mai wakiltar Delta ta kudu a majalisar dattawa ta Nijeriya. Kotun karkashin jagorancin mai shari’a C.O Onyeabo ta yanke wannan hukumcin ne a ranar Asabar.

 

Hukumar zabe ta Nijeriya INEC ta ayyana Manager a matsayin wanda ya lashe zaben karkashin jam’iyyar PDP, amma tsohon gwamnan jihar Emmanuel Uduaghan ya kalubalanci nasarar da ya samu. Sai dai Lauyan Emmanuel, Mr. Thomson Okpoko, ya fada wa kotun cewa an tafka magudi sosai a yayin zaɓen 23 ga watan Fabrairu, 2019. Sai lauyan ya yi kira ga kotun da ta soke zaben.

 

Bayan tattara bayanai, mai shari’a Onyeabo ya soke zaben, sannan ya bukaci hukumar zabe ta kasar da ta sake sabon zabe cikin watanni uku. Kazalika, kotun ta kuma bukaci hukumar zaben da ta amshe takardar lashe zaben da ta ba Mr Manager, inda ta jaddada cewa wanda aka yi karar ya gaza kare kansa bisa zargin badakalar aringizon kuri’un da aka yi ma sa.

 

Da ya ke magana da jaridar The Punch  bayan yanke hukuncin, lauyan James Manager, Mr Larry Selekeowei (SAN) ya ce ba su yi farinciki da hukuncin ba, amma dai za su yi nazari kansa daga bisani su daukaka kara.

 

 

Punch:        Jani/Banye

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply