Home Sabon Labari Dino Melaye na tika rawa saboda matsalar da APC ta shiga

Dino Melaye na tika rawa saboda matsalar da APC ta shiga

112
0

Tsohon Sanatan jihar Kogi ta Yamma Dino Melaye ya fitar da wani faifan bidiyo a yammacin Alhamis din nan yana tika rawa, yana murna. Makasudin bidiyon shi ne murnar rikicin cikin gida da jam’iyya mai mulkin Nijeriya ta APC ta shiga.

Kazalika Dino Melaye ya rinka ambatar sunan Adams Oshiomhole yana nuna farin cikinsa a kan dakatar da Oshiomhole din da kotu ta yi daga shugabantar APC.

Dino Melaye dai ya samu matsala da jam’iyyar APC kafin zaben 2019 daga bisani kuma jam’iyyar ta kayar da shi zabe bayan da ya koma PDP. Shin ya kuke kallon wannan murna da Dino Melaye ke yi?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply