Home Kasashen Ketare Dogaro da kai: Karin matasa 115 za su koyi sana’o’in hannu a...

Dogaro da kai: Karin matasa 115 za su koyi sana’o’in hannu a Sokoto

94
0

Gwamnatin jihar Sakkwato ta soma bayar da wani horon sana’o’in hannu ga matasa 115 da aka zaɓo daga ƙananan hukumomin jihar 23.

Manufar bayar da horon ga matasa ita ce, don su koyi sana’o’in da za su dogara da kai har su taimaki ƴan uwa da abokan arziƙi.

Matasan dai za su share tsawon makonni biyu suna karɓar horon.

Horon haɗin guiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Sakkwato da asusun kula da yawan jama’a na majalisar ɗinkin duniya UNFPA.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply