Home Coronavirus Dokar hana fita ta haddasa cinkoson gawarwaki a Lagos

Dokar hana fita ta haddasa cinkoson gawarwaki a Lagos

110
0

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya koka da cewa gawarwaki sun cike wuraren ajiye gawa na jihar.

Da yake bayani a gaban ƴan jarida a ranar Asabar, ya ce cinkoson gawarwakin da aka samu ya biyo bayan rashin binne gawarwakin da dokar hana fita ta janyo.

Sai dai ya yi kira ga jama’ar jihar da suka rasa ƴan uwansu, da suje su fara shirin binne su, domin dokar hana fitar ba ta shafi binne gawarwaki ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply