Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta tara Naira milyan 1.9 a cikin kwanaki biyu na makon da ya gabata daga kudaden da take cin mutanen da suka keta dokar kullen coronavirus tara.
Kwamishiniyar Shari’a Aisha Dikko ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar. Ta ce akasarin masu laifin an kama su da laifin kin sanya takunkumin rufe hanci, face mask, da kuma fitowa waje ba tare da kwakkwaran dalili ba.
Gwamnatin ta ce ga duk wanda aka samu ya fito waje babu dalili kuma bai sanya face mask ba to ana karbar Naira 5,000 a matsayin tara daga wurinsu, yayin da wadanda kuma suka ki martaba barin tazara a tsakaninsu da sauran jama’a ake karbar Naira 7,000 a wurinsu. Kazalika ta ce wani lokacin ma gwamnati za ta iya kwacewa mutum abin hawarsa ya koma mallakin gwamnati.
