A Asabar din na, al’umar jihar Kaduna za ta sake shakar iskar ‘yanci daga kullen da aka tilasta mata don rigakafin yaduwar cutar kwaronabairos.
Za a fita daga karfe takwas na safe, a koma karfe shida na yamma sannan an ware kasuwanni na unguwa a makarantun firamare mafi kusa, da jama’a za su iya zuwa sayayyar kayan abinci ba sai an yi tattaki zuwa kasuwanni da ke nesa ba. Da ma gwamnatin jihar Kaduna ta ware laraba da asabar don a dinga fita daga kulle.
