Home Labarai Dole a hada hannu don ceto ilimin Arewa daga durkushewa

Dole a hada hannu don ceto ilimin Arewa daga durkushewa

134
0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga masu ruwa da tsayi na yankin Arewa, da su bada gudunmuwa domin ceto bangaren ilimin yankin daga koma bayan da yake.

Tambuwal ya yi wannan kira ne a lokacin da kwamtin shugabannin jami’o’i suka kai masa ziyara a jihar Sokoto.

Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya fitar, ya ce sun zo ziyarar ne domin yi masa ta’aziyyar marigayi Inuwa Abdulkadir wanda shi ne uban jami’ar jihar Sokoto.

A jawabinsa tun da farko, shugaban tawagar Janar Muhammadu Magoro, mai murabus, ya yi wa gwamnan da sauran jama’ar jihar ta’aziyyar daya daga cikin ‘yan kwamitin watau marigayi Abdulkadir.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply