Home Labarai Dole a yi garamawul ga tsari kiwo lafiyar Nijeriya – IHVN

Dole a yi garamawul ga tsari kiwo lafiyar Nijeriya – IHVN

72
0

Cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta Nijeriya ta yi kiran samar da garambawul a tsarin kiwon lafiyar Nijeriya ta yadda zai yaki cutuka da barkewar annoba.

Shugaban cibiyar Dr Patrick Dakum ya yi kiran a raar Alhamis lokacin da yake jawabi a taron Covid-19 na Media Trust.

Ya ce rashin shirin ko ta kwana kan annobar cutuka, ya taimaka wajen dagulewar alโ€™amura ga tsarin kiwon lafiyar wanda dama yake da koma baya.

Dr Dakum ya ce saurann hanoyin da za a farfado da bangaren kiwon lafiyar sun hada samar da tsarin aiwatar da ayyuka a bangaren ta ko wane fanni, kara yawan kudinn da ake ware wa bangaren a kasafin kudin kasa da kuma daina bada fifiko a wasu bangarori tare da watsi da wasu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply