Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Dole ne a rage farashin mai – NLC

Dole ne a rage farashin mai – NLC

102
0

Shugaban kungiyar Kwadagon Nijeriya NLC Ayuba Waba ya yi kiran da a sake bitar rage farashin man fetur a Nijeriya.

Waba ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a birnin Jalingo na jihar Taraba, yana mai cewa karin kudin man wata hanyace ta tatse aljihun ‘yan Nijeriya tare da azurta wasu tsirarun ‘yan kasuwar mai.

Waba ya yi bayanin cewa babu dalilin kara farashin man a daidai lokacin da farashin danyen man bai tashi ba a kasuwar duniya, wanda kuma wannan shi ne dalilin da ‘yan kasuwar suka bada na rage farashinsa tun farko.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply