Home Labarai Dole ne Diezani ta dawo Nijeriya don ta fuskanci hukunci – EFCC

Dole ne Diezani ta dawo Nijeriya don ta fuskanci hukunci – EFCC

66
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC ta bukaci kasar Birtaniya da ta dawo da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke gida Nijeriya.

Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu ya yi wanna kira a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a Kaduna.

Ya ce ya zama wajibi a dawo da tsohuwar ministar ta domin ta fuskanci zarge-zargen da ake mata na sace kudaden Nijeriya dala biliyan biyu da rabi.

Magu, ya yi zargin cewa akwai wasu taron barayin dukiyar kasa da ke taimakawa Diezani, wanda ya ce hakan ba abu ne mai kyau ga ci gaban kasa ba.

Ya kara da cewa hukumar EFCC na aiki da hukumomin duniya don tabbatar da maido da tsohuhar ministar gida.

Shugaban hukumar, ya ce tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 hukumar ta yi nasara kan shari’o’i 1,266 da suka shafi cin hanci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply