Gwamnatin jihar Kano ta umurci shugabannin makarantun sakandare na kwana a jihar da su koma cikin harabar makarantun da zama ko a kore su daga aiki.
Kwamishinan ilmi na jihar Sanusi Kiru ne ya ba da umurnin a Kano.
Yace ana so kowane faransifal ya koma da zama a cikin harabar makarantar da ya ke shugabanta domin tabbatar da tsaron rayukan dalibai.
Sanusi Kiru ya kuma umurci da a aike da ‘yan sintiri na “Vigilante” a dukkanin makarantun fadin jihar don kara inganta tsaro a makarantun.
